PLAY PODCASTS
Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

29 episodes

Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani

May 9, 202618 min

Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria

May 2, 202620 min

Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar

Apr 25, 202620 min

Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar

Apr 19, 202618 min

Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana

Apr 14, 202620 min

Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........

Apr 4, 202620 min

Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya

Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..............

Mar 14, 202620 min

Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin Najeriya

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ tare da Michael Kuduson a wanan mako ya yi duba kan wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

Jan 31, 202620 min

Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu. Gabanin fuskantar wannan lamari dai hatta yanayin damina da lokacin zuwanta ya sauya daga abinda aka saba da shi, batun da hatta a wasu wuraren da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya ma an shaida hakan. Tuni dai wannan al’amari na sauyin lokutan yanayin zafi da damina ko kuma sanyi ya zama abin tattaunawa a tsakanin jama’a dangane da dalilan da suka janyo hakan, da dai wasu sauran tambayoyi da ake da ƙishirwar neman amsoshinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman............

Jan 11, 202620 min

Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Michael Kuduson..........

Dec 13, 202520 min

Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a wasu sasaan Jamhuriyar Nijar. A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake aikin noma don ganawa da jama'a, sannan da samun sauran tarikicen da manoman suka bari a gonakansu. Sai dai a irin lokacin na komawar makiyayan ana samun rikicin dake faruwa ' tsakaninsu da manoman da ba su ida tattare Kayan da suka noma ba, kuma da yanda wasu makiyayan ke saurin komowa a lokacin da manoman ke tsaka da aiki, duk da an tanadi dokar da ta tsaida komi a kasar ta Nijar.

Nov 29, 202520 min

Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil

An buɗe taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya za su mayar da hankali da kuma samar da dabaru kan sauyin yanayi. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala.

Nov 15, 202520 min

Yadda wani ruwa da ke ɓulɓulowa ta ƙasa ke zubar da gidaje da kashe bishiyu a Nijar

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan yau zai maida hankalin ne kan wani ruwan dake bullowa daga kasa Wanda ya yi sanadiyar zubewar gidaje da kashe bishiyoyi da ga gurbata hanyoyi a unguwar Garin Malam ta Damagaram a Jamhuriyar Nijar. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

Nov 8, 202520 min

Barazanar wutar daji da ke lakume gonakai a Jamhuriyar Nijar

A cikin wannan shirin ,za mu leko Jamhuriyar Nijar inda a duk shekara ake fuskantar barazanar wutar daji da ke lakume gonakai da cimaka. Hukumomin Nijar sun dau matakai domin kawo karshen wannan al'amari da manoma da kuma jama'a ke kuka a kai.

Nov 1, 202520 min

Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya

Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba. Wannan lamari dai ya tayar da hankalin waɗannan manoma, waɗanda sun sauya alƙibla ne saboda ganin yadda farashin amfanin gona dangin hatsi ya faɗi warwas a kasuwanni, kuma sun yi haka ne domin su more daga ribar da aka yi ta ci daga barkono, amma sai gashi lamarin ya yi musu ta leƙo ta koma. A kusan ilahirin kasuwannin kayan gwari, gani za ka yi ga barkono, wanda kafin yanzu yake tamkar gwal, sai ga shi yanzu masu saye su na mai tayin da suka ga dama. Masana sun yi ittifakin cewa, ba shakka rashin tsari da alƙibla wajen noma da kuma binciken halin da kasuwa ke ciki sun taka rawa ainun a wcikin wannan matsala da aka samu. Sai dai kuma, matsaloli na yanayi ma sun taka irin nasu rawar, domin akwai matsin lamba daga yadda tsarin ruwan sama ya sauya, da sauraan matsaloli da suka addabi ƙasar noma. Matsalar yanayi da muhalli na mummunan tasiri akan ko wane irin nau’i na noma. shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin, tare da Michael Kuduson.

Oct 25, 202520 min

Masana game da fallen da ke bai wa ɗan Adam kariya daga sinadaran hasken rana

A wannan makon, shirin zai mayar da hankali ne akan wani rahoton da masana suka fitar, wanda ke nuna cewa fallen nan ko shimfidar da ke bai wa ɗan Adam kariya daga wasu sinadaran hasken rana masu haɗari, da ake kira Ozone Layer, wanda kafin yanzu ake bayyana damuwa a game da lalacewar da ya fara yi, sakamakon ayyukan da ɗan Adam ke aiwatarwa ya fara gyaruwa. Sai ku biyo mu domin za mu tattaunawa da masana, shehunnan malamai akan wannan maudu’i. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin 'MUHALLINKA RAYUWARKA' tare da Michael Kuduson.......

Oct 19, 202520 min

Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya

Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam. bayanai sun ce wannan cibiyar bunƙasa noma na ƙunshe da tarin kayakin buƙata a lokacin noman walau na rani ko kuma na damuna duk dai a ƙoƙarin haɓaka harkar noma a jihar ta Arewa maso yammacin Najeriya. Bankin Musulunci da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kanon ne suka samar da wannan cibiya wadda ta laƙume biliyoyin dalolin Amurka ƙarƙashin shirin KSSB na haɓaka noma bisa kulawar SASAKAWA. Ku latsa alamar tsari don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.....

Oct 11, 202519 min

Yadda manoma a Jahuriyar Nijar suka koma noman Gyaɗa da Gujiya gadan-gadan

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda manoma a Nijar suka koma noman Gyaɗa da riɗi gadan-gadan bayan sun yi watsi da shi tsawon shekaru, saboda matsaloli da noman ke fuskanta.Maraɗi ce kan gaba a noma Gyada ko Gujiya shekaru aru aru, sai Zinder da kuma Doso, waɗanda suka taimaka wajan hada-hadar kasuwancin Gyaɗa har a Kano inda ake tattara Dalar Gyadar.Yawan noman Gyadar ne ma ya sa turawan mulkin mallaka suka kafa masana’antar sarrafa man Gyada a 1943 a Maraɗi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........

Sep 27, 202520 min

Ƙorafin makiyaya a Jigawa kan yadda ake saida filayen kiwo

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan wata matsala da ta kunno kai tsakanin makiyaya da manoma a yankin ƙananan hukuomin Guri da Kiri Kasamma da kuma Kaugama na jihar Jigawa a Arewacin Najeriya, inda Fulani makiyaya suka koka kan yadda aka salwantar da wuraren kiwon dabbobinsu da wurin shayar da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........

Sep 20, 202520 min

Yadda jihar Jigawa ta ɗauki matakin daƙile sare bishiyoyi barkatai

A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ta'adar sare bishiyoyi barkatai ke tasamma karewar wasu bishiyoyi da ke da mutukar amfani ta fuskar tattalin arziki da kuma samar da kayan marmari, a gefe guda kuma hakan na barazana ga muhalli. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

Sep 6, 202520 min

Yanayin ƙuncin da manoman masara a Tarayyar Najeriya suka shiga

Shirin namu na wannan mako zai yi duba ne kan yanayin ƙuncin da manoman masara a Tarayyar Najeriya suka shiga a kasar, a dalilin tallafin rancen inganta noman masara da gwamnati ta basu ta hannun bankuna wanda ake kira Anchor borrowers.

Aug 30, 202520 min

Yadda damunar bana tazo da tasgaro ga manoma a wasu jihohin Arewacin Najeriya

A wannan makon, shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Micheal Kuduson yayi duba ne kan yadda damunar bana tazo da tasgaro ga manoma a wasu daga cikin jihohin Arewacin Najeriya musamman jihar Kano duba da cewa har zuwa wannan lokaci wasu ba su kai ga yin noma ba, ko kuma ba su jima da farawa ba. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......

Aug 23, 202520 min

Rashin fitar shuka ya zame wa wasu manoma ƙalubale a Jamhuriyar Nijar

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya tattauna a kan rashin fitar shuka a farkon daminar bana, lamarin da ya zame wa manoma ƙalubale babba a Jamhuriyar Nijar, matsalar da suka fara fuskanta tun daga farkon daminar bana.

Aug 16, 202520 min

Yadda jihar Yobe ke ƙoƙarin rage rashin ayyukan yi tsakanin matasa ta hanyar habbaka noma

Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka na wannan makon zai yaɗa zango ne a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda duba da cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin jihar Yobe, inda kusan kashi 90% na al’ummar jihar ke harkar noma da kiwo. Gwamnatin jihar ta kaddamar da mataki na biyu na rabon kayan aikin noma domin kara samar da abinci da karfafa tattalin arzikin cikin gida tare magance rashin ayyukan yi tsakanin matasa da zummar magance barazanar matsalolin tsaro da shigar matasa kungiyoyin ‘yan ta’adda. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson

Aug 9, 202518 min

Illar da maganin ciyawa ke yiwa amfanin gona idan ba'a yi amfani da shi yadda ya dace ba

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya mayar da hankali ne kan illar da maganin ciyawa ke yiwa manoma, idan aka yi rashin sa'a ko kuma aka yi kuskure a yadda ya kamata a yi feshinsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

Aug 2, 202520 min

Tsadar takin zamani a Najeriya na barazana ga harkar noma a daminan bana

Shirin Muhalllinka Rayuwarka na wannan makon ya yi duba ne kan tsadar takin zamani da ake samu Najeriya, lamarin da masana harkar noma ke cewa an kama hanyar fuskantar tsadar kayan abinci ko karancinsa. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Michael Kuduson..............

Jul 26, 202520 min

Shirin gwamnatin Jigawa na farfado da noman yankin Sahara a jihar

Tun a karshen watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki, wato shekarar 2025, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da shirin noman na yankin sahara karamar hukumar Maigatari dake masarautar Gumel. A jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da shirin, gwamnan jihar, Umar Namadi ya ce an kirkiro shirin ne don bunkasa noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma rage kwararar mutane daga kauye zuwa birane.

Jul 19, 202520 min

Samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a arewacin Najeriya

Jul 13, 202520 min

Yunƙurin gwamnatin jihar Nasarawa a Najeriya na haɓaka noma da sarrafa rogo

Jul 5, 202519 min